san turakin kazaure Engr. Ahmad Rufa'i Zakari ya ziyarci ƙaramar hukumar gwiwa domin gabatar da ta'aziyyar rasuwa da kuma dubiyar marassa lafiya.
Yau assabar 9/sept/2023 tunda safiyar ranar mai girma san turakin kazaure Engr. Ahmad Rufa'i Zakari ya ziyarci ƙaramar hukumar gwiwa domin gabatar da ta'aziyyar rasuwa da kuma dubiyar marassa lafiya.
Idan a cikin wannan ƙaramar hukumar ya ziyarci garuruwa kamar haka;
- Indirawa.
- Gwiwa.
- Wailare.
- Buntusun duzau.
Sannan ya gabatar da ta'aziyya ga chairman party na ƙaramar hukumar gwiwa Abdullahi Adamu wanda akayiwa rashi.
Mai girma san turakin kazaure ya gabatar da wannan ziyarce ziyarce ga al'umma da waɗanda iftila'in ruwa ya faɗawa.
Alhamdulillah yayi addu'a ubangiji (SWT) ya jiƙan waɗanda suka mutu, Marassa lafiya Allah ya basu lafiya.
Waɗanda iftila'in ruwa ya faɗawa Allah ya tsare gaba.
.jpeg)


Comments
Post a Comment