Posts

Showing posts from August, 2023

.

.

Me zai hana sojojin Nijar su miƙa mulki a wata 9? - Tinubu

Image
  Jagoran ƙungiyar Ecowas kuma shugaban Najeriya Bola Tinubu ya shawarci sojojin da ke mulki a Nijar, su mayar da ƙasar kan turbar dimokraɗiyya a cikin wata tara, kamar yadda Najeriya ta yi a shekarun 1990. Wata sanarwa da fadar shugaban Najeriyar ta fitar na cewa a zamanin Janar Abdulsalami Abubakar cikin 1998, an kafa kwamitin miƙa mulki cikin wata tara, kuma kwamitin ya yi nasarar mayar da ƙasar kan tafarkin dimokradiyya. Don haka, Shugaba Tinubu ya ce bai ga dalilin da zai sa a kasa yin haka a Nijar ba, matuƙar sojojin da suka yi juyin mulki a ƙasar, da gaske suke yi. Tinubu na wannan jawabi ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Majalisar Ƙoli kan Harkokin Addinin Musulunci ta Ƙasar a ƙarƙashin jagorancin Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji sa'ad Abubakar lll. ''Mai Alfarma, kada ka gaji don Allah, za ka sake koma wa Nijar. Ba za a amince da halayyar sojojin ba. Idan suka yi sauye-sauye cikin gaggawa, to mu ma cikin hanzari za mu sassauta takunkuman da muka ƙaƙ...

Ana ƙarancin kwaroron roba a Kenya

Image
  Kenya na fama da karancin kwaroron roba da take rabawa kyauta ga maza saboda ragin tallafi da take fuskanta daga kungiyoyi. Ƙasar na bukatar akalla kwaroron roba miliyan 400 a kowacce shekara. Gwamnati a yanzu na iya raba kwaroron roba miliyan 150 ne kacal, wanda bai kai rabin abin da ake bukata ba. Gidauniyar AIDS Foundation, ta yi gargaɗin cewa idan ba a shawo kan matsalar ba, Kenya na iya fuskantar kalubalen yaɗuwar cututtuka irinsu HIV, da cutar da ke yaɗuwa ta jima'i da ɗaukar cikin da ba a so. Wani babban jami'i a hukumar da ke yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ya ce akwai bukatar ɗaukan matakai a cikin gaggawa. Ƙwararru a fannin lafiya da 'yan majalisa da ƙungiyoyin tallafi za su gudanar da wani taro nan da kwanaki uku a birnin Mombasa domin shawo kan matsalar da kuma samar da karin magungunan HIV.

.

.